Zulum ya dakatar da ma’aikatan asibiti baki daya bayan ya kai ziyarar bazata ya tarar babu kowa a asibitin

0
548

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya dakatar da duka ma’aikatan babban asibitin Ngala saboda sun ki fita aiki su duba marasa lafiya.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa garin Ngala wanda aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram a shekarar 2015 shine helkwatar karamar hukumar Ngala, wadda ke da hanyoyi daban-daban da suka shiga wasu kasashen nahiyar Afrika da suka hada da Cameroon, Chad, Sudan da kuma Central Afrika.

Mai magana da yawun gwamnan jihar, Malam Isa Gusau, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce matakin da gwamnan ya dauka ya biyo bayan wata ziyarar bazata da ya kai asibitin, inda ya iske iya ma’aikatan NGO ne kawai suke duba marasa lafiya.

Gusau ya ce wadanda lamarin ya shafa, sun hada da; likitoci, ungozomomi, masu bayar da magani, masu bincike da sauran su.

“Gwamnan bai ji dadi ba ganin yadda ake kara samun marasa lafiya, amma ace babu ma’aikacin gwamnati ko daya da yaje asibiti a ranar,” cewar Gusau.

“Wannan asibitin gwamnatin jihar Borno ne, amma abin takaici babu wani ma’aikacin gwamnatin jiha ko daya da yazo don duba marasa lafiyar nan, kuma duka mun biya su albashin su.

“Wadannan ma’aikatan jin kai na NGO, taimakawa ma’aikatanmu ya kamata suyi ba wai suyi aikin baki daya ba.

“Ina umartar hukumar lafiya ta jihar Borno da ta dakatar da duka ma’aikatan wannan asibitin.

‘Zan dawo wannan asibitin, ina fatan zan ga canji akan abinda na gani yau,” Gusau ya bayyana abinda Zulum ya ce.

A lokacin da yake garin na Ngala, gwamnan ya ziyarci makarantu guda uku inda ya bayar da umarnin gyara ajujuwan da ‘yan ta’adda suka lalata.

Haka kuma ya bayyana shirin shi na mayar da ‘yan gudun hijira zuwa garuruwan da suke makwabtaka da garin irin su Logumani da Gajibo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here