Zan kara aure da ‘yar fim ku taya ni zaben wacce ta dace dani – In ji Sani Mu’azu tsohon gwamnan kwana 90

0
1371

Sani Mua’azu tsohon jarumi a masana’antar Kannywood da Nollywood da yake fitowa a matsayin uba a mafi yawancin fina-finai, wanda kuma a yanzu aka fi saninsa da tsohon gwamnan Alfawa a cikin shirin ‘Kwana Casa’in’, a wannan karon ya zo da wata almara da ta ja hankalin mabiya shafukan Kannywood.

Jarumin ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Twitter, inda ya ce yanzu haka yana da mata wacce ba ‘yar fim bace a taya shi dubawa wajen zaba masa zankadediyar budurwa da ta dace da shi a cikin kyawawan ‘yammatan Kannywood domin kara karfafa dangantakar aiki.

Haka kuma ya kara da jaddada cewa yana so mutane suyi tunani sosai, domin kuwa shi ba da wasa yake ba, ga dai abinda jarumin ya rubuta:

‘Ina da mata guda daya, kuma ita ba ‘yar fim ba ce. Idan har zan sake auren mace ta biyu daga masana’antar fim dan kara karfafa dangantakar aiki, wacce kuke ganin ya kamata na aura, a tsakanin kyawawan jaruman da kuka sani. Kuyi tunani da kyau domin kuwa wannan ba da wasa nake ba.

Koda wallafa wannan rubutu na shi, mutane sun yi ta bashi amsa inda wasu ke bayyana matan da suke ganin sun dace da shi, amma kuma mafi yawancin mutanen sun fi zaba mishi Fulanin shi ta cikin shirin Kwana Casa’in, inda suke cewa sun fi dacewa.

Bayan daukar lokaci da karbar ra’ayoyin jama’a ya sake wallafa cewa:

“Mu cigaba da tattaunawa, amma ina da wani tsokaci da zanyi. Ina matukar son matata wacce ba ‘yar fim ba, ita ce asalin gimbiya ta, mahaifiyar ‘ya’yana guda uku. Ya batun yadda za ta damu, ko kuna ganin ba wani matsala? Me kuke gani? Musamman ma ‘yammata, me zaku ce akan hakan?

Ana dai ta bashi shawarwari akan ya janye kudirinsa domin farin cikin matarsa tunda shima yana tunanin halin da za ta shiga. Inda wasu kuma ke cigaba da kawo masa samfurin kyawawan ‘yan matan da ake ganin sun dace da shi.

Shin a ganinku wace jaruma ce ta dace da shi, tun da dai ya ce ba wai da wasa yake ba?

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here