Zamu sake sanya dokar hana fita nan da mako biyu – Gwamnatin tarayya

0
541

A jiya Litinin ne kwamitin gudanarwa ta yaki da cutar COVID-19, ta nuna damuwa akan yawan yaduwar cutar da ake samu tsakanin manyan jami’an gwamnati, inda ya ce cutar na shafar gwamnati da kuma fannin tsaro na kasa.

Shugaban kwamitin kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya bayyana hakane a wajen taron da kwamitin ta saba gabatarwa a Abuja, inda ya ce akwai yiwuwar a kara sanya dokar hana fita domin dakile cigaba da yaduwar cutar.

Mustpaha, ya shawarci manyan Najeriya da su dauki wannan cuta ta COVID-19 da gaske, ya ce cutar ba ruwanta da mulki ko mukami.

Gargadin Mustapha ya zo ne bayan kara samun yaduwar cutar da ake yi tsakanin gwamnoni da kuma wasu manya na gwamnati. Gwamnonin da suka kamu da cutar a kwanan nan sun hada da gwamnan Ebonyi, David Umahi; gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa; da kuma gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu.

Da yake yiwa masu mukamin gargadi, Mustapha ya ce: “A ‘yan kwanakin nan mun samu karin mutane da suke manya a gwamnati da suka kamu da cutar. Wannan yana da babbar matsala ga gwamnati da kuma tsaron kasa. Muna rokon kowa ya lura ya kare kanshi daga wannan cutar, cutar babu ruwanta da mulki ko mukami.”

Da aka tambayeshi ko za a kara sanya dokar hana fita a wannan karon, Mustapha ya ce abubuwan da za su faru nan da makonni masu zuwa su za su sanya a yanke hukuncin abinda ya kamata ayi.

Ya ce: “Ba za mu iya cewa ga abinda zai faru nan gaba ba, amma zamu yi kokari wajen kare rayukan ‘yan Najeriya.

“Domin samun damar hakan, idan har ta kai ga sai an sake rufe al’umma baza mu ji kunyar yin hakan ba. Za mu sanar da shugaban kasa, wanda zai yi duba akan rahoton ya yanke hukuncin abinda ya kamata ayi. Abin da zai faru nan da mako biyu zuwa uku shi zai sanya mu san abinda ya kamata ayi.”

Mustapha ya ce kuma mambobin kwamitin sun gana da shugabannin hukumomin tsaro na kasa a jiya Litinin.

Ya ce ganawar tayi duba akan yadda za a sanya mutane su bi dokokin da aka gindaya dangane da cutar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here