Zamu sake garkame Masallatai da Coci – Gwamnatin tarayya ta gargadi ‘yan Najeriya

0
2512

Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa za ta iya canja dokar bude wuraren ibada da tayi matukar mutane ba su bi dokokin da ta gindaya ba.

Sakataren gwamnatin tarayya kuma shugaban kwamitin gudanarwa na COVID-19, Boss Mustapha, shine ya bayyana haka a jiya Alhamis a wajen taron da kwamitin ta saba gabatarwa a kowacce rana.

Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya tuni ta fitar da dokokin da ta gindaya ga masu zuwa wuraren ibada a kowanne jihohi.

Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta na so shugabannin addinai su bi wadannan dokoki da ta gindaya.

“Bin dokokin yana da matukar amfani domin gujewa fadawa wani hali ta hanyar sanya rayukan al’umma cikin hadari na kamuwa da cutar ta coronavirus.

“Muna so kowa yayi hankali ya bi doka yadda ya kmata.

“Kwamitin PTF za ta cigaba da lura da yadda abubuwa za su cigaba da gudana akan dokar.

“Bayan haka baza mu bata lokaci ba wajen duba akan lamarin, domin rage yaduwar cutar.

“Dole a sanya dokokin a kananan hukumomi, domin samun sauki wajen bin diddigi idan an samu wadanda suka kamu da cutar.”

Ya ce yana da matukar kyau jihohi su gabatar da kamfan don wayar da kan al’umma wajen magance yaduwar cutar, haka kuma ya kara da cewa cibiyoyin addinai dana gargajiya suma suna da rawar da za su taka wajen wayar da kan al’umma game da cutar.

Haka kuma Mustapha ya shawarci ‘yan Najeriya akan amfani da maganin da hukumar lafiya ta duniya ba ta amince da shi ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here