Zamu kori hafsoshin tsaron da suke wasa da rayukan al’umma – Sanata Ahmad Lawan

1
2441

A jiya Lahadi ne shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana cewa duk wani shugaban tsaro da ya kasa tabuka komai a Najeriya za a kore shi.

Ahmad Lawan, wanda yayi hira da manema labarai na gidan gwamnatin tarayya bayan kammala ganawa da shugaba Buhari a fadar shugaban kasa, ya ce majalisar a shirye take ta karbi kudadane da za ta tinkari matsalar tsaro a Najeriya, ciki harda daukar karin jami’an tsaro daban-daban a Najeriya.

Ya ce dole ne a samar da kayayyakin aiki da zasu karfafa guiwar jami’an tsaro wajen yakar ‘yan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas, da kuma ‘yan bindiga a fadin Najeriya.

Lawan wanda ya ce matsalar tsaro a Najeriya, musamman a yankin Arewa na bukatar a bawa jami’an tsaro kayan aiki, inda ya kara da cewa shugabannin tsaro na kasar nan dole su tashi tsaye su kawo karshen wannan matsalar a cikin lokacin da aka gindaya musu.

“Ba zai yiwu mu cigaba da zama ba tare da sanya lokacin da za a magance wadannan matsaloli.

“Kun san kasar na fuskantar kalubale sosai na tsaro, kuma na zo ne don na tattauna da shugaban kasa akan maganar da muka yi dashi a baya na cewa zamu bi kowacce hanya don inganta yanayin tsaro a Najeriya.

“Mun yi imani majalisar dattijai da ta wakilai ta kasa za ta karbi wasu kudade don magance muhimman bukatun dake a cikin hukumomin tsaro na kasar nan domin mu karfafa hukumomin, da basu damar yakar ‘yan Boko Haram a Arewa maso Gabas, da kuma ‘yan bindiga a fadin kasar.

“Abu na biyu shine, majalisa ta yadda cewa muna bukatar karin jami’an tsaro irinsu sojan kasa, sojan ruwa, sojan sama, ‘yan sanda, da sauransu.

“Sashe na 14 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya tabbatar da cewa manufar gwamnati za ta kasance ne wajen samar da tsaro da walwalar jama’a.

“Saboda haka bamu da wani zabi wanda yafi mu magance kalubalen tsaron dake gaban mu.

“Ina ganin dole mu fadawa kanmu gaskiya, matsalar tsaro a kasar nan musamman a Arewa, na bukatar mu bawa jami’an mu kayan aiki.

“Haka kuma hafsoshin da suke shugabantar wadannan hukumomi dole ne su tashi tsaye, maganar gaskiya ma dole mu sanya musu wa’adi na lokacin da za a kawo karshen wannan matsalar.

“Ba zai yiwu mu dinga zama sakaka ba, ba tare da sanin lokacin da matsalar za ta kare ba.

“Idan muka bayar da tallafi kuma muka tarar wani bai yi aikin da ya kamata ba, dole ne zamu kore shi daga ofis. Saboda rayuwar ‘yan Najeriya tafi komai, saboda haka ita zamu bawa muhimmanci fiye da komai. Na tabbata a yau abinda yafi damun gwamnati a yanzu shine kawo karshen matsalar tsaro.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here