Hukumar hada fina-finai ta Najeriya (NFVCB) ta ce za ta nemo mutanen da suka yi shirin fim din madigo da ake shirin fitar da shi kwanan nan mai suna ‘Ife’, idan har basu kai wa hukumar tace fina-finai ba.

Babban daraktan hukumar Adebayo Thomas, ya bayyanawa manema labarai a ranar Laraba cewa: “Dokar kasa ta hana irin wannan abu.

“Idan har suna Najeriya, sai mun nemo su.

“Hadda wadanda ke da hannu a ciki suma.

“Kafin ka sanya kanka a cikin irin wannan abu dole akwai wadanda za su dauki nauyi.

“Idan kun ce kuna daukar shirin fim na ‘yan madigo, shikenan wannan ne aikin ku.

“Amma mu bai zo gare mu ba.

“Idan har ya zo wajen mu zamu san cewa wannan shine abinda ya kamata muyi.”

Da take mayar da martani akan wannan fim din a shafinta na Twitter, furodusar fim din, Pamela Adie, ta bayyana cewa Ife fim ne na soyayya ba wai iskanci aka yi a ciki ba.

“Don gujewa kokwanto, ‘IFE’ fim ne na soyayya.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here