Za mu kashe mazajenku da ‘ya’yanku mu barku cikin talauci – ‘Yan bindiga suka sanar da ‘Yan Kauye

0
3534

“A karamar hukumar Goronyo, ‘yan gudun hijira 500 ne da ‘yan bindiga suka raba da gidajensu suka kafa sansani a wasu kangon gidaje.

“Sama da watanni 11 kenan zawarawan suna rayuwa ne ta hanyar zuwa su nemo ita ce su sayar, yayin da duka mazajen da matayen suke zaune cikin bakin talauci, kamar dai yadda ‘yan bindigar suke so,” cewar daya daga cikin wakilan Daily Trust.

Tun da farko dai anyi tunanin samar da matsugunni ga mutanen da ambaliyar ruwa a shekarar 2010 ta rutsa da su a Goronyo, a yanzu haka gidajen da aka yi watsi da su, sun zama sansanin mutane 500 da ‘yan bindiga suka raba da gidajen su a Malanfaru, Riyojin Tsamiya da kuma kauyen Kamitau dake karamar hukumar ta Goronyo.

A cikin zawarawa 50, 28 sun rasa mazajensu sanadiyyar harin ‘yan bindigar. Dukkansu dole ta sanya su shiga daji su nemo ita ce su sayar domin samun kudin abinda za su ciyar da kansu da ‘ya’yansu da sauran muhimman abubuwan bukata.

“A lokacin da ‘yan bindigar suka kawo hari kauyen mu, wasu mata ciki hadda ni mun gudu cikin daji, bayan mun dawo na tarar da gawar mijina a cikin mutane 21 da aka kashe,” cewar Azima mai shekaru 25 da take shayarwa. “Jaririna kwanakinsa arba’in kacal a lokacin da aka kashe masa mahaifinsa.”

“Jaririna watan shi daya kacal a duniya a lokacin da ‘yan bindigar suka kawo harin suka kashe mutane 21, ciki hadda mijina. Bayan na gano gawarshi, sai nabi sauran matan kauyen mu muka yi tafiyar kilomita 30 zuwa wannan sansanin,” cewar Hindatu Bawa.

A sansanin rayuwar babu dadi, akwai matsalar abinci, ruwan sha da kuma matsalar tsaro da suke damun ‘yan gudun hijirar a Goronyo, muamman ma da hare-haren ‘yan bindigar yayi kamari.

“Dole ta sanya mu shiga daji muyi tafiya mai nisan gaske don neman itacen da zamu sayar mu ciyar da kanmu. Haka muke yi domin mu samu mu rayu,” cewar Hindatu.

“Muna barin sansanin mu da misalin karfe 9 na safe, sannan mu dawo da yamma,” cewar wata bazawara mai suna Jimmai Ibrahim mai shekaru 40.

Idan sun fita da sa’a Jimmai ta kan samo itace na N600, wani lokacin kuma na N400 a kullum.

“Muna sayar da itacen a cikin sansanin mu,” cewar ta.

Kudin da take samu da shi take amfani wajen lura da ‘ya’yanta guda biyar a sansanin.

“Muna bukatar abinci da kayan sawa ga ‘ya’yanmu. Muna bukatar taimako a wannan lokaci,” ta ce.

Ita kuwa Zainabu Abu, wata bazawara a cikinsu, haduwarta da ‘yan bindigar sun nuna mata yadda rayuwarta za ta kare.

“A lokacin da ‘yan bindigar suka shigo, sun same ni a waje, inda shugaban su ya ce mu mazajenku da ‘ya’yanku muke so mu kashe, sannan mu saka ku cikin talauci,” ta ce. “Sun kone gidajen mu sun kashe mazajen mu.”

Ita da wasu matan da suka samu tsira sunyi tafiyar kimanin awa 4 kafin su iso wannan sansani na Goronyo suka cigaba da zama cikin talauci kamar yadda ‘yan bindigar suka bayyana mata.

Mai magana da yawun sansanin ‘yan gudun hijirar, Sama’ila Garba, ya ce wasu daga cikinsu sun koma kauyukansu da zama saboda wahalar rayuwa a sansanin, sun gwammace koma mene zai same su ya same su a gidajensu.

“Muna da iyalai a nan, kuma muna buga-buga wajen ganin mun samawa iyalan mu abinda za su ci,” ya ce. ‘Ni dai acaba nake yi, inda wasu kuma daga cikin mu suke shiga gari suna neman aikin yi.”

Garba wanda yake samun kimanin N500 a kowacce rana, ya ce “Muna cikin tashin hankali, muna bukatar taimakon gwamnati, musamman ma a fannin tsaro. Kullum muna samun labarin ana kashe mutane a kauyukan dake makwabtaka damu, kuma babu wanda ya damu ya lura damu.”

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here