Za mu hukunta duk Malamin Islamiyyar da ya bude makaranta – Gwamnatin jihar Kano

0
640

A wata hira da kwamishinan ilimi na jihar Kano, Sunusi Maji Dadin Kiru, yayi da da gidan rediyon vision dake jihar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar baza ta sassautawa duk wanda ta kama ya karya dokar bude makarantu ba.

Kwamishinan ya bayyana hakane a lokacin da yake amsa tambayoyi game da batun komawa makaranta, inda ya ce za su hukunta duk wani Malamin Islamiyya da aka kama shi da hannu wajen bude makaranta a fadin jihar.

Ya ce bude makarantun islamiyyoyi a wannan lokacin zai sanya rayuwar mutane musamman ma ta daliban cikin hadari, inda yayi gargadi ga Malaman akan kada su sake su bude makaranta har sai gwamnatin jihar ta basu dama.

Ya ce: “Duk wanda muka kama da hannu wajen karya dokar da muka sanya za mu dauki hukunci a kansa mummuna.”

A daya bangaren kuma gwamnatin tarayya tayi gargadi ga gwamnonin jihohi akan suyi watsi da matsin lambar da iyayen yara suke saka musu wajen bude makarantu.

Gwamnatin tace ba karamin hatsari bane a bari daliban su koma makaranta a wannan lokacin, inda ta ce amma daliban da suke shirin zana jarrabawar WAEC da NECO lokaci na nan zuwa da za a barsu su koma makarantu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here