Za mu cigaba da bincike akan badakalar Sanusi Lamido – Ganduje

0
464

Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa hukumar yaki da cin hanci ta jihar za ta cigaba da bincike akan tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II.

Gwamnan ya bayyana haka ne a jiya lokacin da yake hira da manema labarai a gidan gwamnatin jihar dake Kano.

Gwamnan yana amsar tambaya ne akan kirkirar masarautu hudu a jihar da kuma sabbabin dokokin masarautar.

“Kwarai kuwa, akwai matsaloli na doka da suka jinkirta canjin da muka yi kokarin kawowa, amma yanzu da yake babu tsohon Sarkin, kotunan sunyi watsi da wadannan dokoki, kuma yanzu hukumar hana cin hanci tana da ikon cigaba da bincike akan tsohon Sarkin bisa ga doka,” cewar shi.

Ganduje ya kara da cewa a wancan lokacin akwai wata kungiya ta Dattawan Kano, wadanda suka yi kokarin su kawo cikas ga wannan tsari na gyara, inda ya ce suma kotu tayi watsi da karar su, saboda haka basu da hurumin dakatar da su a lokacin.”

Ya ce bayan sun kammala kawo karshen matsalolin, sai suka cigaba da aikin su har suka kammala, inda ya kara da cewa babban dalilin yin wannan kwaskwarima a masarautar shine domin samar da cigaba a wasu sassa na jihar.

Haka kuma gwamnan yayi magana akan shirin da gwamnatinsa take yi na cigaba da aiwatar da ayyukana cigaba tare da la’akari da tabarbarewar tattalin arzikin da cutra COVID-19 ta haifar.

Game da wannan tsarin, ya ce daya daga cikin matakin da zai dauka shi ne rage kasafin kudin jihar da kashi 30 cikin dari, ya kara da cewa tuni har an fara duba game da kasafin kudin, yayin da za ayi amfani da wannan kudi wajen gabatar da wasu ayyukan.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here