Za a samu yawan mace-mace a Najeriya saboda asibitoci sun daina karbar marasa lafiya – Gwamnatin tarayya

0
127
  • Gwamnatin tarayya tayi gargadin samun yawaitar mace-mace a Najeriya a ‘yan kwanakin nan
  • Gwamnatin ta bayyana haka ne ganin yadda asibitoci suka daina karbar marasa lafiya indai ba masu cutar Coronavirus bane
  • Gwamnatin ta ce a halin yanzu tana iya bakin kokarinta wajen samar da maganin wannan cuta ta coronavirus, amma kuma dole akwai ka’idoji da ya kamata abi kafin fara bawa al’umma

Gwamnatin Najeriya tayi gargadi akan yiwuwar samun yawaitar mace-mace a Najeriya, saboda asibitoci basa karbar marasa lafiya indai ba masu cutar Coronavirus ba.

Sakataren gwamnatin tarayya, kuma shugaban kwamitin masu lura da cutar coronavirus ta Najeriya, Boss Mustapha, shine ya bayyana haka a wajen taron kwamitin na 32 da aka gabatar jiya a Abuja.

Haka kuma yace an samu gudummawar N792,121,613.89 daga wajen ‘yan Najeriya a ranar 14 ga watan Mayu, inda yace akwai wadanda suka bayar da gudummawar naira daya (N1).

“Mun lura da raguwar marasa lafiya a asibitoci. Idan ba a manta ba ministan lafiya ya bukaci cibiyoyin lafiya da kada suyi wasa wajen lura da marasa lafiya da suke bukatar taimako.

“Saboda haka PTF tana kira ga asibitoci da su taimaka su cigaba da karbar marasa lafiya domin rage cututtuka a Najeriya. A yadda muke gani a yanzu, akwai yiwuwar samun yawaitar mace-mace a Najeriya saboda asibitoci sun daina karbar marasa lafiya indai ba masu cutar Coronavirus bane,” cewar Mustapha.

Yace a halin yanzu suna iya bakin kokarinsu wajen ganin an samar da maganin cutar, amma dole sai an bi ka’idoji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here