Ministan lafiya, Osagie Ehanire, ya ce yawaitar masu cutar COVID-19 a Najeriya, hakan wani gargadi ne dake nuni da cewa za a kara samun yawaitar mace-mace a Najeriya.
Ministan ya bayyana hakane jiya Alhamis a Abuja, lokacin yake magana da kwamitin gudanarwa ta COVID-19.
Sai dai ministan ya ce akwai matakan da za a dauka don magance faruwar hakan.
Ya ce: “Tunda yawancin wadanda suke mutuwa ‘yan sama da shekara 50 ne ko kuma masu cutar siga, ko hawan jini, ciwon koda ko kanjamau; wadannan mutanen dole a basu kulawa ta musamman.
“Kulawar da za a basu ta hada da kare daga kusantar wajen da masu cutar suke ta hanyar sanyasu su zauna a gida; sanya takunkumi a koda yaushe.
“Sannan za a hana su zuwa wuraren da akwai yawaitar jama’a, kamar irinsu kasuwanni, wuraren ibada da sauransu.
“Duk wanda aka tabbatar da cewa yana da cutar ba za a bari ya zauna a gida ba dole ne a kai shi cibiyar kula sa masu cutar a lokacin da aka fara ganin alamun cutar a tare da shi.
“Jinkiri na iya zama matsala, saboda cutar na iya canjawa tayi muni a kowanne lokaci ba tare da anyi tsammani ba.
“Tare da wadannan muhimman matakan, zamu iya rage yawan mace-macen dake tunkaro mu.
“Wannan annobar har yanzu tana tare damu kuma mutane na ta kamuwa da ita a kowacce rana, ciki kuwa hadda manya a kasar nan.
“Har sai ta wuce zamu cigaba da bin umarnin hukumomin lafiya na zuwa wuraren da yake akwai taron jama’a.”
Ehanire ya bayyana cewa za a tura masana zuwa cibiyoyi domin su gwada ingancin sabon maganin cutar na COVID-19 da aka samu a ‘yan kwanakin nan.
Ya kuma ce Najeriya ta rattaba hannu akan wata yarjejeniya da kasar Koriya ta Arewa a fannin kiwon lafiya da kuma fannin kimiyya ta lafiya.
Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:
Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa
Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa
Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com