Za a iya daukar coronavirus a wurin jima’i ko kuma a jikin maniyyi – Sabon bincike

0
223

Wani sabon bincike ya nuna cewa mutanen da suka warke daga cutar Coronavirus su nesanci yin jima’i domin gudun kada su gogawa wasu cutar ta maniyyi din su.

Wasu marasa lafiya ‘yan kasar China da suka warke daga cutar, an samu kwayar cutar a jikin maniyyi din su bayan an gabatar da gwaji a kai, kamar dai yadda jaridar Telegraph ta kasar Birtaniya ta ruwaito.

Wannan sabon bincike da aka samu ya sanya masana a fannin kimiyya cikin damuwa, inda suke ganin cewa cutar ka iya shiga jikin mutane ta hanyar jima’i, hakan ya sanya suka bukaci mutane da su nesanci jima’i na tsawon wani lokaci bayan an tabbatar da sun warke daga cutar.

Daya daga cikin marasa lafiyan a asibitin Shangqui Municipal dake jihar Henan, an samu cutar a jikin maniyyi din shi, kwanaki 16 bayan ya kamu da cutar, sannan kuma an sake samun cutar a jikin maniyyin nashi kwanaki uku bayan ya warke.

“Amfani da kwaroron roba zai iya zama wata hanya da mutum zai iya kare kanshi da iyalanshi daga kamuwa da wannan cuta,” cewar bincike, kamar yadda aka wallafa a mujallar kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasar Amurka.

Sai dai kuma wasu masanan sun bayyana cewa wannan bincike da aka gabatar akan mutane 38 yayi kadan, inda a iya maniyyin mutane 6 kawai aka samu cutar.

Zuwa yanzu dai masanan sun samu cutar a jikin maniyyin mutane 27 a fadin duniya.

Sai dai kuma har ya zuwa yanzu ba a tabbatar da shigar cutar jikin maza ko yana iya zama matsala ga kwayayen haihuwarsu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here