Annobar Coronavirus ta canja komai a duniya a wannan lokacin. Duk abubuwan da bamu taba tunanin zasu faru ba sun zama ba komai ba a yanzu. Manyan Masallatai masu albarka na duniya duka an kulle su.
Mun ga mutane n mutuwa saboda cutar da har yanzu ba a gano mafita a kanta ba. Mun daina zuwa Masallaci, mutane da yawa sun kwashe watanni ba tare da gabatar da sallar juma’a a jam’i ba. Mun gabatar da azumin watan Ramadana a kulle a cikin gidajen mu. Yanzu kuma lokaci yazo da sallar idi din ma baza ta samu ba.
Sallar idi na da matukar muhimmanci ga Musulmai, amma a wannan karon komai ya canja, babu sallah, babu kwalliya da aka saba yi, babu bikin sallah da sauransu.
A wata sabuwar dokar hana fita da kasar Saudiyya ta saka, ta ce za ta fara aiki daga gobe Asabar 23 ga watan Mayu zuwa ranar 27 ga watan Mayu a yayin da cutar ke kara kamari a kasashen Musulmai, hukumomin kasar sun sanya dokar hana fitar ta awanni 24 ba tare da sassautawa ba.
Hukumomin kasar dai sun bayyana karbar tarar Riyal 10,000, a wajen duk wanda aka kama ya karya wannan dokar, kimanin Naira miliyan daya kenan a kudin Najeriya.
A yankin gabas ta tsakiya, kasar Saudiyya ita ce kasar da tafi jigata da cutar ta Coronavirus fiye da sauran kasashen. Inda birnin Makkah yafi ko ina masu dauke da cutar a kasar.
Har ya zuwa yanzu dai kasar ta Saudiyya ba ta yanke hukunci akan aikin Hajji ba, wanda za a gabatar dashi a watan Yuli, inda miliyoyin mutane za su hadu don su bautawa Allah.