Za a bude Masallatai sama da 90,000 ranar Lahadi a kasar Saudiyya

0
829

Bayan shafe sama da watanni biyu a kulle, ma’aikatar dake kula da addinin Islam ta kasar Saudiyya, sun shiga aikin shara da tsaftace Masallatai 90,000 a kasar, inda ake shirin bude su a ranar Lahadi.

Sai dai Masallatan dake birnin Makkah basu daga cikin wadanda za a bude.

A rahoton da Saudi Gazette ta ruwaito, za a bude Masallatan ne bisa bin ka’idojin da ministan addinin Musulunci na kasar, Dr. Abdullatif Al-Asheikh ya bayar da kuma wasu manya masu fada aji a kasar.

Ma’aikatar ta fara gabatar da shirin wayar da kan jama’a akan yadda za su bi doka wajen kula da kansu a wuraren ibada, ma’aikatar ta wallafa wannan sanarwa a gidajen talabijin, gidajen rediyo, jaridu, jaridu na yanar gizo, da kuma shafinsu na yanar gizo.

Daga cikin dokokin da aka sanya a kasar sun hada da yin alwala daga gida, wanke hannu da kyau kafin fita daga gida da kuma bayan dawowa gida. Tsofaffi da kuma wadanda basu da lafiya an bukaci su dinga gabatar da sallolinsu a gida. Haka an bayar da damar karatun Al-Qur’ani amma da wayar hannu ko kuma mutum ya shiga Masallaci da Qur’aninsa.

Haka kuma an bukaci a dinga zuwa da abin sallah idan mutum yana da hali, sannan kuma dole kowa ya bayar da tazarar mita biyu tsakaninsa da dan uwansa a lokacin sallah.

Haka kuma an hana zuwa da yara da suke kasa da shekaru 15. Tilas ne kowa ya sanya takunkumi, sannan kuma babu musabiha tsakanin Masallata a cikin Masallaci.

Yayin da ita kuma ma’aikatar addinin Islama tayi iya bakin kokarinta wajen tsaftace masallatan da kuma sanya magunguna da zasu kare mutane daga kamuwa daga cutar a fadin kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here