Yawan ‘yan Najeriya da suke jira su saci kudin Najeriya sun fi yawan wadanda suke sata yanzu – Dino Melaye

0
574

Tsohon sanata mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Sanata Dino Melaye ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana halin da Najeriya take ciki.

Dino ya bayyana cewa Najeriya na cikin wani hali, saboda akwai mutane masu yawan gaske da suke jira su samu damar da za su saci kudin al’umma.

Ya ce: “A Najeriya yawan mutanen da suke jira su samu damar da za su saci kudin na Najeriya na al’umma yafi yawan mutanen da suke cikin gwamnati a yanzu suke satar kudaden jama’a. Muna cikin tashin hankali.”

View this post on Instagram

God pass through Nigeria

A post shared by Senator Dino Melaye (SDM) (@dinomelaye) on

A makon da ya gabata Press Lives ta kawo muku rahoton yadda aka sha tataburza da tsohon sanatan, bayan an bukaci ya sayar da kadarorinsa ya taimakawa al’ummar yankinsa da kudin.

Dino ya bayyana cewa kudin da yake dashi ba zai iya ciro ‘yan Najeriya daga halin da suke ciki ba, inda ya ce matukar ya sayar da kadarorinsa to talaucewa zai yi.

A karshe ma dai sanatan ya bayyana cewa yana addu’a Allah ya kara masa arzukin da zai kara siyan kadarori, saboda su yafi so a rayuwar shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here