Yawan masu Coronavirus ya kai miliyan 1 a kasar Brazil bayan mutane 54,771 sun kamu a rana daya

0
278

Kasar Brazil ta zama kasa ta biyu a duniya da mutum sama da miliyan daya suka kamu da cutar Coronavirus bayan kasar Amurka.

A ranar Juma’a da daddare, ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayyana cewa mutane 54,771 sun kamu da cutar a cikin kwana daya, wannan dai shine yawan mutanen da ba a taba samu ba a duniya sai a wannan karon, inda hakan ya daga yawan masu cutar zuwa mutum 1,032,913.

Jami’an lafiyar kasar sun ce rabin mutanen da suka karu sun kamu da cutar ne saboda sakaci da suka yi wajen kai rahoto a jihohi uku na kasar ciki kuwa hadda Sao Paulo.

Bayan haka kuma akwai sama da mutum 1,200 da suka mutu a kwanaki hudu a jere, inda yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa mutum 49,000.

Al’umma sun yo caa akan shugaban kasar Jair Bolsonaro, akan yadda yake sakaci da wannan cuta a kasar.

Shugabannin kungiyoyi daban-daban sun yi arangama da gwamnonin jihohi da shugabannin gargajiya, akan dokar da suka sanya mai tsauri wajen dakile yaduwar cutar. Haka kuma wannan sakaci da shugaban kasar yayi ya sanya ministocin lafiya guda biyu sunyi murabus.

Kasar Amurka dai ita ce take da mafi yawan mutane da suke da cutar a duniya, inda sama da mutane miliyan 2.2 suka kamu da cutar, sannan kuma ita ce take da mafi yawan mutanen da suka mutu, an tabbatar da mutuwar sama da mutum 120,000 a kasar ta Amurka.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here