Wata kotun majistire dake Yaba a jihar Legas ta saki wata yarinya ‘yar shekara 16 mai suna Timilehin Taiwo, wacce aka gurfanar a gaban kotu da laifin kashe wani mutumi mai suna Babatunde Ishola mai shekaru 51 da yayi kokarin yi mata fyade.

Linda Ikeji ta ruwaito rahoton yadda Timilehin ta cakawa Babatunde wuka, a yankin Aboru dake jihar ta Legas a ranar 7 ga watan Maris.

A bayanin da ta yiwa ‘yan sanda, Timihelin ta ce, mutumin wanda yake abokine a wajen mahaifinta, ya kira zuwa cikin gidanshi ta taimaka masa wajen diban ruwa, yayin da yake zama shi daya a gidan, ta ce dama can ta saba taimaka masa da aikace-aikacen gida. Ta ce a ranar da lamarin ya faru a lokacin da take taimakawa mutumin sai yayi kokarin yi mata fyade. Ta ce a kokarin kare kanta, sai ta dauki wuka ta caka masa, hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Daga baya ‘yan sanda sun mika Timilehin zuwa gaban kotu da laifin kisa.

Da yake sauraron karar a jiya Laraba, mai shari’a Philip Adebowale Ojo, ya cire laifin kisan daga kan Timihelin bayan shawarar da ya samu daga ma’aikatar shari’a ta jihar Legas.

Daraktan ofishin kare hakkin wadanda ake kara na jihar Dr Babajide Martins, wanda ofishinsa ya kare wacce ake karar, ya nuna farin ciki da hukuncin da kotun ta yanke akan Timihelin.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here