‘Yar shekara 10 ta sha alwashin sanya farin ciki a zuciyar yara irinta a wannan lokaci na Korona, inda take raba kayan wasa ga yara

0
297

Wata karamar yarinya ‘yar shekara 10 ta sha alwashin sanya farin ciki a zuciyar yara irinta a wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus aka hana zirga-zirga.

Yarinyar mai suna Chelsea Phaire dake garin Danbury ta aika da akwatunan kayan wasa guda 1,500 don karfafa guiwar yara irinta da suke zaune a gida a wannan lokaci.

A cikin kowacce akwati akwai abubuwan rubutu, irinsu kala, takardu da dai sauransu, an rabawa yaran ta hanyar kaiwa gidan marayu da makarantu, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Mahaifiyar yarinyar mai suna Candance Phaire, ta ce diyar tasu tana yawan rokarsu akan za ta bude gidauniya ta taimako tun tana ‘yar shekara bakwai a duniya.

“Ta nace, kowanne wata sai ta tambaya, ‘yaushe za mu fara gidauniyar Chelsea?’ A lokacin da ta cika shekara 10 ta kara tambayar mu, sai muka ga ya dace ta fara,” cewar mahaifiyarta.

An ruwaito cewa an bude gidauniyar yarinyar a ranar murnar haihuwarta a watan Agustan shekarar 2019, inda ta dinga rokar abokananta akan su bayar da gudummawa maimakon kyautar da za su ba ta ta murnar ranar haihuwa.

Da wannan gudummawa da ta samu, ta aika da akwatuna guda 40 na farko ga wasu yara marasa galihu. A cikin watanni biyar ita da mahaifiyarta sun bayar da kusan akwatuna 1,000 ga yara.

Daya daga cikin kungiyar da ta samu tallafin Chelsea ita ce kungiyar James Storehouse, wacce kungiya ce dake taimakon marayu ta hanyar tallafa musu wajen karatu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here