‘Yar sanda ta bindige mijinta saboda baya daga wayarta idan ta kira shi

0
678

Wata jami’ar ‘yar sandar kasar Kenya da aka bayyana sunanta da APC Maureen, yanzu haka tana nan tana wasan buya da jami’an tsaro, bayan ta harbi mijinta sau biyu da bindiga mai kirar AK-47 a yankin Dago dake Nyalenda, bayan wani rikici ya hado su.

Babbar jami’ar ‘yar sandan dake yankin gabashin Kisumu, ana zarginta da harbin mijin nata saboda yana bawa mai aikinsu kudin abinci ba tare da ya sanar da ita ba, sannan kuma baya daga wayarta idan ta kira shi.

Wani rahoton ‘yan sanda da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya bayyana cewa mijin matar ma’aikacin asibiti ne a Kisumu, inda ya samu ciwuka a gefen kanshi sakamakon harbin, ya bayyana cewa lamarin ya faru a lokacin da yake kallon talabijin.

Rahoton ‘yan sandan ya ce:

“Ta tsaya a bakin kofa rike da bindigar AK-47. Ta sanar da shi cewa za ta kashe shi sannan ta kashe kanta, ai kuwa sai ta harbe shi har sau biyu a gefen kanshi.

“Bayan nan sai ta gudu, inda har yanzu ba a san inda take ba, bayan ta dawowa da daya daga cikin abokanan aikinta bindigar.”

K2TV ta ruwaito cewa an kai mijin matar zuwa wani asibiti a Kisumu, inda aka yi masa magani aka sallame shi.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here