‘Yar Aljannah: Uwargida ta taimakawa mijinta wajen nemo mata kishiya a yayin da ta dauki ciki

1
1934

Mata da yawa baza su taba yadda su bari wata ta kwanta da mijinsu ba. Ba ma maganar kwanciya ba, akan magana kawai sai mace ta haukace idan taga mijinta yana magana da wata.

Maganar gaskiya ma, mata suna ganin duk wata mace dake mu’amala da mijinta a matsayin babban kalubale a gareta da kuma aurenta. Amma hakan ba yana nufin duka suka taru suka zama daya ba.

A yayin da wasu matana suke tada hankalinsu a lokacin da mijinsu yayi musu kishiya, sai gashi wata mata ‘yar kasar Malaysiya ta taimakawa mijinta wajen nemo masa amarya a lokacin da ta dauki ciki, inda ta ce ta kasa jurewa ta ga mijinta cikin wani halin da babu wanda zai kula dashi, saboda tana dauke da ciki ita kuma baza ta iya kula dashi ba.

Wannan lamarin dai ya faru a Shah Alam, dake kasar Malaysia, inda matar mai suna Khuzatul Atiqah ta nemowa mijin nata mai suna Samuel Dzul amarya a lokacin da ta dauki ciki. Ta ga cewa mijinta na dawowa a gajiye daga wajen aiki a kullum, amma kuma duk da haka shine yake yin aikin gida, kuma ya kula da ita, inda ita kuma take fama da tsohon ciki.

Saboda tsananin soyayyar da take yiwa mijin nata, Khuzatul ta kasa jurewa halin da mijinta yake ciki. Kawai sai ta fara nemo masa amarya wacce za ta kula da shi, saboda ita baza ta iya ba.

Da ta tambayeshi ko yana son ya sake aure, Samuel kawai yayi dariya, saboda shi bai taba tunanin sake aure ba, amma kawai ta fara nemowa mijin nata amarya.

Ta nemowa mijin nata wata mata da ta rabu da mijinta mai suna Nur Fathonah, a matsayinta na bazawara Fathonah ita ce ta dace da zama matar Samuel ta biyu.

Fathonah tayi mamaki sosai a lokacin da ta samu sako daga Khuzatul akan tana so ta auri Samuel, ba ta taba tunanin za ta sake aure ba. Amma daga baya ta amince da auren Samuel.

Bayan auren matan guda biyu sun zauna lafiya, inda ta zama bababr kawa ga Khuzatul. Haka ita ma Fathonah ta samu farin ciki a wannan gida. Yanzu haka duka su ukun sun yanek shawarar kula da junansu da kuma taya Samuel cigaba da kasuwancinsa.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here