Yanzu-yanzu: ‘Yan Boko Haram sun yiwa soja da dan sanda kinsan gilla a wani sabon bidiyo

0
640

Ana ta korafi a shafukan sadarwa a Najeriya biyo bayan sakin wani bidiyo da ‘yan kungiyar Boko Haram suka yi dake nuna yadda suka yiwa wani soja da dan sanda yankan rago a yau ranar dimokiradiyya.

‘Yan Boko Haram din sun kashe wadannan jami’an tsaro ne kwanaki kadan bayan sun kai hari sun kashe mutane 81 a kauyen Foduma Kolomaiya dake jihar Borno.

Bidiyon ya nuna dan sandan da sojan a durkushe suna bayyana ainahin sunayensu da kuma yadda ‘yan Boko Haram din suka kama su.

Jami’an tsaron da aka harbe sun bayyana cewa suna kan hanyarsu ta Monguno daga Maiduguri, inda ‘yan ta’addar suka yi musu kwanton bauna suka kama su, inda suka kira su da ‘Sojojin Tilafa’.

“Sunana Corporal Emmanuel Oscar, mai lamba 13NA/70/8374, ‘yan Tilafa sun kama ni a kan hanyar Monguno zuwa Maiduguri,” cewar sojan.

Ana shi bangaren, dan sandan, wanda yayi magana da yaren Hausa ya ce: “Sunana Yohanah Kilus, ni dan sanda ne ina da mukamin Inspector.

“An kama ni tsakanin hanyar Maiduguri zuwa Monguno; yanzu haka ina hannun sojojin Tilafa,” ya bayyana kafin ‘yan bindigar guda biyu su harbe su shi da sojan.

A ranar Talatar nan ne Daily Trust ta ruwaito yadda ‘yan bindigar suka kashe sojoji guda a wani hari da suka kai sansanin sojojin dake kauyen Auno cikin jihar Borno.

Sai dai kuma shugaban hukumar sojin na Najeriya, Laftanal Kanal Tukur Buratai, wanda ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ana samun gagarumar nasara akan yaki da ‘yan ta’addar a yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Haka shi ma shugaban kasar a bayanin da yayi na ranar dimokaradiyya ya bayyana cewa matsalar ‘yan bindiga da ta’addanci ta samu koma baya sosai a kasar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here