Yanzu-yanzu: ‘Yan Boko Haram sun shiga kauyen Goni suna cin karensu ba babba a jihar Borno

0
995

A yanzu haka ‘yan Boko Haram suna cikin garin Goni Sulemanti dake karamar Nganzai dake jihar Borno suna cin karen su babu babba.

Duk da dai mazauna garin sun bayyana cewa sun sanar da jami’an tsaro akan wannan abu dake faruwa, amma sun ce har ya zuwa yanzu ‘yan ta’addar suna cikin garin suna yawo abin su.

Har ya zuwa yanzu dai ba a san ainahin irin barnar da ‘yan bindigar suka yi ba.

Ku cigaba da kasancewa tare damu zamu kawo muku cikakken bayani.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here