Yanzu-yanzu: ‘Yan Boko Haram sun kashe sojoji 20 a jihar Borno

0
399

Akalla sojoji 20 ne suka rasa rayukansu, inda da yawa kuma suka ji muggan raunika a lokacin da wasu da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne suka yi musu kwanton bauna a jihar Borno ranar Talata, wata majiya ta bayyanawa Daily Trust.

Sai dai kuma, hukumar soji ta ce iya sojoji biyu kawai aka kashe a harin.

Haka kuma ta kara da cewa sojojin sun kashe ‘yan Boko Haram 17 a wannan karon batta da aka yi.

An ruwaito cewa lamarin ya faru akan babbar hanyar Damboa zuwa Maiduguri, kimanin kilomita 30 daga garin na Damboa.

Wata majiya ta hukumar tsaro ta bayyanawa wakilan Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun budewa sojojin wuta, inda suka yi sanadiyyar mutuwar sojojin da yawa.

“Abin takaici sojojin mu da suka fita aiki akan hanyarsu ta dawowa garin Damboa kimanin kilomita 30.

“Yan bindigar suka yi musu kwanton bauna suka fara harbinsu ta ko ina.

“Mun rasa mutane masu yawan gaske.

“Gawarwakin sojojin da suka mutu an kai su Maiduguri tare da wadanda suka ji raunika.

“Yanzu haka suna karbar magani a asibitin sojoji,” cewar majiyar.

Sai dai kuma, helkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar soji ta Lafiya Dole, a ranar 7 ga wata, ta kashe ‘yan Boko Haram 17 a wannan kwanton bauna.

A wata sanarwa da Manjo-Janar John Enenche ya fitar a ranar Laraba, ya ce iya sojoji biyu ne kawai suka mutu, inda hudu kuma suka ji raunika.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here