Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 69 sun kuma kone kauye a Borno

0
1221

Wasu ‘yan bindiga da ake tunanin ‘yan Boko Haram ne, sun koma kauyen Foduma Kolomaiya yau Laraba da safe, inda suka sanyawa kauyen wuta kasa da awa 24 bayan kashe mutane 69 a cikin kauyen, cewar wata majiya.

‘Yan bindiga sun kashe mutane 69 a kauyen, wanda yake da nisan kilomita 11 daga garin Gazaure, dake karamar hukumar Gubio dake cikin jihar ta Borno a jiya Talata.

Karamar hukumar Gubio dake da nisan kilomita 96 daga garin Maiduguri, gari ne dake arewacin jihar Borno.

Wani mazaunin kauyen ya bayyanawa Daily Trust cewa, harin wanda ‘yan bindigar suka kai da rana, sun shafe awa biyu a cikin garin kafin su fita.

Bayan kashe mutanen da suka yi, ‘yan bindigar sun kashe shanu sama da 300, sannan suka sace kimanin shanaye 1000.

An gano cewar ‘yan bindigar sun kara komawa kauyen a yau Laraba da safe, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi kafin su sanyawa gidaje wuta.

Photo Source: Daily Trust

A cewar wani jami’in tsaro da ya bukaci a boye sunanshi, ‘yan bindigar sun koma kauyen da misalin karfe 6 na safiyar yau Laraba.

“Mun samu kiran waya yau da safe cewar ‘yan bindigar sun koma kauyen da aka kashe mutane masu yawa ranar Talata.

“Bazan iya cewa komai game da lamarin ba, amma jami’an mu za suyi bayani dalla-dalla,” cewar jami’in tsaron.

Wasu ‘yan kungiyar sa kai sun bayyanawa wakilin Daily Trust cewa, akwai yiwuwar mutane da yawa sun sake asarar rayukansu a wannan hari na safe da aka kai.

“Mutanen kauyen suna kokarin binne wadanda aka kashe mu da safiyar yau, sai ‘yan bindigar suka dawo bayan kashe kimanin mutane 70 a jiya.

“Sun iso kauyen nan da misalin karfe 6 na safe suka fada kan mutane da harbi.

“Sun kone gidaje da dama a cikin kauyen yanzu,” cewar majiyar ta ‘yan sa kai da suka bayyanawa wakilin Daily Trust a waya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here