Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun kashe mutane 13 a jihar Katsina

0
1391

Akalla mutane 13 ne suka mutu sanadiyyar wani hari da ‘yan bindiga suka kai wasu kauyuka dake karamar hukumar Faskari cikin jihar Katsina.

Kauyukan sun hada da Unguwar Gizo, Maigora, Sabon Layi da Mai Ruwa.

Wata majiya ta ce ‘yan bindigar sun shiga garin da tsakar dare don su saci dabbobinsu.

Sai dai kuma, mutanen kauyen sunce sam basu yarda ba, suka tinkari ‘yan bindigar aka yi bata kashi.

“A yanzu maganar da nake daku da safiyar nan ta Juma’a muna wajen jana’izar mutane 13 da aka kashe,” cewar mutumin.

“Haka kuma mutane bakwai sunji muggan raunika suna asibiti yanzu suna karbar magani.”

“Haka an harbi wani mutumi a kafa shi ma a kauyen Mai Ruwa,” ya kara da cewa.

Da yake tabbatar da kai harin, kakakin rundunar yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya ce; “kwarai gaskiya ne, an kashe mutane 13.”

“Mun sha gayawa mutane musamman wadanda suke gaba-gaba da su guji tinkarar ‘yan bindiga, saboda suna dauke da manyan bindigogi, kuma baza ku iya yakar su da adduna da wukake ba.

“Sun je satar shanu ne sai ‘yan kauyen suka tinakre su, su kuma ‘yan bindigar suka far musu da harbi,” cewar kakakin rundunar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here