Yanzu-yanzu: ‘Yan bindiga sun je har cikin fada sun kashe mai gari a jihar Katsina

1
5393

A safiyar Litinin din nan ne wasu ‘yan bindiga da ba a san daga inda suke ba sun shiga har fadar Mai garin ‘Yantumaki, Abubakar Atiku Maidabino, dake karamar hukumar Danmusa, sun harbe shi.

Wasu majiyoyi daga jihar sun ruwaito cewa ‘yan bindigar sun afka garin akan babur ne, inda suka kai hari fadar da misalin 12 na dare, suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi.

Daga baya ‘yan bindigar sun shiga cikin fadar mai garin suka harbe shi, sannan suka yiwa Dogarin shi guda daya mai suna Gambo Chakau rauni.

Abubakar Atiku Maidabino Photo Source: Daily Trust

An bayyana cewa za a gabatar da jana’izarsa da misalin karfe 11 na rana a fadarsa.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce daga baya ‘yan bindigar sun tsre cikin daji, wadanda lamarin ya shafa kuma an garzaya da su asibitin Danmusa.

“Muna cigaba da gabatar da bincike,” cewar shi.

Wannan dai na zuwa ne kwana daya bayan kashe shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani, da ‘yan bindigar suka yi a jihar ta Katsina.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here