Yanzu-yanzu: Wata jiha a Najeriya ta bawa dalibai damar komawa makaranta a mako mai zuwa

0
1138

Gwamnan jihar Cross River, Ben Ayade, ya ce duka makarantu gwamnati za su koma aiki a ranar 16 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa babban mai bawa gwamnan jihar shawara a fannin sadarwa, Christian Ita, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Calabar.

Gwamnan jihar ya shirya tsarin da zai bawa dalibai tsaro ta hanyar da baza su kamu da cutar ba idan sun koma makaranta, cewar Legit.ng.

Gwamnan ya ce zai raba kayan kariya ga daliban kyauta, sannan kuma zai rabar da su ga wasu jami’o’in jihar.

Gwamnan ya ce gwamnatin jihar ba ta so ta cigaba da kallon dalibai suna cigaba da zama a gida, inda yace hakan yana lalaci a garesu.

“Ina ganin ya kamata daliban su koma makaranta, saboda naga haka ya faru a kasar China, inda naga dalibai sun koma makaranta da takunkumi a fuskarsu.

“Saboda haka kowa zai saka takunkumi a fuskarsa idan zai tafi makaranta idan ya isa makaranta zai cire ya sanya makari a fuskarsa, don ya samu isashiyar iska,” cewar Ayade.

Gwamnan ya kara da cewa yanzu lokaci ne da ya kamata gwamnatin tarayya ta tallafawa gwamnatin jihar a yayin da yanzu take samar da kayan kariya da za su taimakawa ma’aikatan lafiya na kasar nan.

Ya ce gwamnatin jihar ta sanya kudi da yawa wajen samar da wadannan kayayyaki, kuma ana amfani da abubuwa masu inganci wajen sarrafa wannan abubuwa, sannan kuma sun dauko ma’aikata daga kasar Indiya.

Gwamnan ya roki gwamnatin tarayya da ta sanya hannu a wannan lamari, inda ya ce wannan abu da yake yi yana daya daga cikin kokarin da gwamnatinsa take na yaki da annobar.

A na shi bangaren kuma kwamishinan ilimi na jihar ya ce wannan komawa da za ayi kamar gwaji ne.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here