Yanzu-yanzu: Wani gwamna ya kamu da cutar coronavirus a Najeriya

0
643

Wani labari da dumi-duminsa da muka samu ya bayyana cewa gwamnan jihar Abiya, Okeazie Ikpeazu, ya kamu da coronavirus.

Kwamishinan yada labarai na jihar, John Okiyi Kalu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya saki ranar Litinin, kamar dai yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Kwamishinan ya kara da cewa tun tuni gwamnan ya riga ya killace kansa, tun gabannin sakamakon gwajin da aka dauka nashi ya fito, inda kuma ya bawa mataimakinsa umarnin hawa kujerarsa kafin ya samu sauki.

John ya ce: “Idan baku manta ba a ranar Asabar, 30 ga watan Mayun shekarar 2020, gwamnan ya bayar da samfurinsa domin a gabatar da gwaji a kai, haka kuma ya umarci mambobin majalisar jihar da kuma na kwamitin yaki da cutar Corona ta jihar da suma su bayar da na su samfurin.

“A ranar Talata 2 ga watan Yuni, sakamakon gwajin gwamnan ya fito kuma lafiyarsa lau a lokacin bai kamu da cutar ba, sai dai kuma a ranar 4 ga watan Yuni, gwamnan ya sake gabatar da samfurinsa domin a sake gabatar da gwaji, a karo na biyun kuma gwajin ya nuna cewa gwamnan ya kamu.”

“Gwamna Okezie ya killace kansa kamar dai yadda hukumar NCDC ta gindaya ga masu cutar suyi, inda kwararrun likitoci suke duba shi a halin da ake ciki yanzu.

“Gwamnan kuma ya umarci mataimakinsa, Ude Oko Chukwu da ya cigaba da gudanar da mulki a jihar daga nan zuwa lokacin da zai samu sauki.

“Saboda haka muna kira ga mutanen wannan jiha da su dauki wannan cuta da gaske domin kuwa gaskiya ce.”

Idan baku manta ba a makon da ya gabata ne shima mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya kamu da cutar, bayan gabatar da gwaji da aka yi a kanshi.

Mataimakin gwamnan shi ma ya killace kanshi jim kadan bayan sakamakon gwajin da aka gabatar a kanshi, kuma an fara bin diddigin wadanda yayi mu’amala da su.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here