Yanzu-yanzu: Shugaban jam’iyyar APC na Arewa, Inuwa Abdulkadir ya rasu

0
374

Babbar jam’iyya mai mulki ta APC ta shiga jimami bayan mutuwar jigo kuma shugaba a cikin Alhaji Inuwa Abdulkadir.

Abdulkadir, ya rasu a yau Litinin din nan, 6 ga watan Yuli, shine tsohon shugaban rikon kwarya na jam’iyyar a yankin arewa maso yamma.

Duk da dai ba a bayyana ko mutuwar ta shi na da nasaba da cutar COVID-19 ba ko a’a, amma majiyoyi da yawa sun rawaito cewa shugaban jam’iyyar bashi da lafiya a safiyar yau Litinin din nan, daga baya kuma ya ce ga garinku nan.

“Eh ba shi da lafiya, kuma ya mutu a safiyar yau Litinin din nan,” wata majiya ta bayyana yayin tabbatar da mutuwar Inuwa, wanda yake yana daya daga cikin mambobin kwamitin jam’iyyar APC.

A wani rahoto makamancin haka, Press Lives ta ruwaito yadda wani babban Malamin addinin Musulunci ya bayyana cewa tilas ne matar marigayi Abiola Ajimobi ta yi zaman takaba na watanni hudu da kwana goma.

Malamin ya bayyana haka ne a lokacin gabatar da addu’ar takwas da aka yi a gidan marigayin, wanda manyan masu fada aji suka halatta.

Malamin kuma ya bayyana cewa duk mutanen da suke yabon marigayin a yanzu, inda a lokacin da yake a raye basu yi ba, sai Allah ya hukunta su.

Ga dai cikakken labarin: Tilas ne surukar Ganduje tayi zaman takaba na kwana 130 – Sheikh Muideen

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here