Yanzu-yanzu: Sarkin Musulmai ya dakatar da sallar idi a fadin Najeriya

7
1196

Mai girma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya umarci a dakatar da sallar idi a jam’i a kauyuka da biranen kasar nan baki daya.

Ya bada umarnin ne a wata sanarwa da ya fitar a yau Alhamis dinnan, wacce sakatare janar na Jama’atul Nasril Islam, Dr Khalid Aliyu ya fitar.

Sarkin Musulmai ya bukaci al’ummar Musulmai da su gabatar da sallar idin su a cikin gidajensu tare da iyalansu ko kuma suyi sallolinsu su daya.

Haka kuma ya bawa gwamnatin jihohin kasar nan da suka bayar da umarnin gabatar da sallar idi a cikin jam’i shawara akan su tabbatar da mutane sun bi dokar da masana a fannin lafiya suka gindaya.

Sarkin ya bukaci gwamnonin da su tabbatar da kowa yabi dokar nisantar juna da aka sanya, sannan kuma kowa ya tabbatar da ya sanya takunkumi da kuma wanke hannu a masallacin idi.

A cewar shi mutane suyi amfani da Masallatai na unguwa domin gabatar da sallar idin a ciki idan har lamarin ya zama tillas sai anyi sallar a cikin jama’a.

Haka kuma Sarkin Musulman ya roki mutane da suji tsoron Allah su kula da kansu domin tabbatar da lafiyar al’umma baki daya.

7 COMMENTS

  1. Magana ta gaskiya wannan badai_dai bane ace anhan mutune gudanar da Sallar Edi sabo da wata Cuta ta Corona virus wadda a zahirance babu ita. Kuma shi Kai Sa’adu kasani cewa Mutane suna daukar ka da mutumcin A matsayin ka na sarkin Musulmai, ammah kuma a yanzu indai harka goyi bayan hana Sallar Edi, a fadin Tarayyar Nigeria to wallahi mutane bazasu Sake ganin kimar kabah don Haka wallahi ka rike girman kah

  2. Sarkin sakkwato qarya kake sallah dai insha allahu se munyi. Daman addinin be dame kuba kuma wallahi girma ya fadi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here