Yanzu-yanzu: Sarkin Kaura Namoda Alhaji Ahmad Muhammad Asha ya rasu

0
176

Sarkin Kaura Namoda, Alhaji Ahmad Muhammad Asha, wanda aka fi sani da Sarkin Kiyawan Kaura Namoda ya rasu a yau Lahadin nan da safe.

Kaninshi, Abdulkarim Ahmad Asha, Dan Jekan Kaura Namoda shine ya sanar da Daily Trust rahoton rasuwar Sarkin, ya sha fama da rashin lafiyar ciwon suga da kuma cutar hawan jini na lokaci mai tsawo.

“An kwashe kwanaki hudu ana yi masa magani a cikin fadarsa a lokacin da cutar ta kama shi. Daga baya aka garzaya dashi asibitin Yariman Bakura, inda Allah ya karbi ranshi a can kwanaki uku bayan an kwantar da shi.”

“Ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, ya bar mata 3 da ‘ya’ya 11, a cikin ‘ya’yanshi akwai Sanusi Muhammad Asha, wanda yake soja ne dake aiki a garin Maiduguri jihar Borno.

“Za a gabatar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, sannan kuma za a binne shi a garin Kaura Namoda,” cewar Abdulkarim.

Wannan dai na zuwa ne kasa da awanni 24 da rasuwar Sarkin Rano, Dr Tafida Abubakar Ila II, daya daga cikin Sarakunan da Ganduje ya nada a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here