Yanzu-yanzu: Sarkin Katsina ya bawa dan bautar kasa sarautar Mai Garin da ‘yan bindiga suka kashe

0
524

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, ya nada Atiku Abubakar Atiku, a matsayin sabon Mai Garin Yantumaki dake cikin karamar hukumar Danmusa dake jihar.

Sabon Mai Garin dai shine babban dan marigayi Atiku Abubakar, tsohon Mai Garin da ‘yan bindiga suka kashe shi a cikin fadarsa kwanakin da suka gabata.

Sakataren masarautar jihar, Sallaman Katsina, Bello Ifo, shine ya tabbatar da haka, inda yace sabon Mai Garin a yanzu haka yana yin bautar kasa ne.

Idan ba a manta ba Press Lives ta kawo muku rahoton yadda ‘yan bindigar suka shiga har cikin fadar Mai Garin suka kashe shi.

‘Yan bindigar sun afka garin da misalin karfe 12 na dare ne akan babura, inda suka dinga harbin kan mai uwa da wabi, daga nan suka wuce kai tsaye zuwa fadar Mai Garin.

Da shigar su fadar suka harbe shi, sannan suka yiwa daya daga cikin Dogarawansa mummunan rauni.

Ga dai cikakken labarin kisan Mai Garin: Yanzu-yanzu ‘yan bindiga sun kashe Mai Gari a jihar Katsina

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here