Yanzu-yanzu: Gwamnatin tarayya ta rage farashin litar man fetur zuwa N121

0
460

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta rage kudin litar man fetur zuwa naira dari da ashirin da daya da kobo hamsin (N121.50).

Hukumar dake da alhakin kula da kuma saita farashin man fetur ta Najeriya, ita ce ta bayyana rage kudin man fetur din daga N123.50 zuwa N121.50.

Sabon farashin ya fito a cikin wata sanarwa da kungiyar masu sayar da man fetur suka fitar a jiya Lahadi 31 ga watan Mayun shekarar 2020.

Ranar 7 ga watan Mayu ne kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya bada sanarwar rage farashin man fetur da ake shigowa da shi daga waje daga N113.28 zuwa N108.00 kowacce lita guda daya.

Bayan samun sanarwar rage kudin man fetur din, PPRA ta bayyana kudurinta na duba akan rage kudin da ‘yan Najeriya za su dinga biya idan sun je shan mai.

Daily Trust ta ruwaito cewa rage kudin man fetur din ya biyo bayan faduwar farashin man fetur da aka samu a kasuwannin duniya sanadiyyar annobar coronavirus da ta addabi al’ummar.

Wannan dai shine karo na uku da kudin man fetur din ya rage kudi a cikin wannan shekara ta 2020.

A ranar 18 ga watan Maris ne gwamnatin tarayya ta bayyana rage kudin man fetur na farko daga N145 zuwa 125 a kowacce lita daya.

Daga baya kuma a ranar 31 ga watan Maris gwamnatin tarayyar ta kara rage kudin man fetur din daga N125 zuwa N123.50 kowacce lita daya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here