Gwamnatin jihar Kano, ta bayar da sanarwar hana hawan babbar sallah da ake shirin gabatarwa a ‘yan kwanakin nan, a kokarin da take na dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar, Comrade Muhammad Garba shine ya bayyana haka ga manema labarai a jihar. A cewar sa, za a gabatar da sallar idi cikin bin dokokin da hukumomin lafiya suka gindaya.

Muhammad Garba ya kara da cewa duka Sarakuna guda hudu na Gaya, Karaye, Bichi da Rano, za su gabatar da sallolinsu a Masarautunsu.

Kwamishinan ya cigaba da cewa, za a sanya abubuwan wanke hannu a Masallatai dake fadin kananan hukumomi 44 na jihar domin amfani da su.

Haka kuma ya kara da cewa za a dauki jami’an gwamnati domin sanya ido akan abubuwan da za su faru a Masarautun guda biyar na jihar domin tabbatar da cewa an bi doka kamar yadda ya dace.

Idan ba a manta ba gwamnatin ta sanya dokoki irin wadannan a lokacin karamar Sallah, duka domin yaki da yaduwar cutar ta coronavirus a jihar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here