Yanzu-yanzu: Gwamnan Bauchi ya dakatar da Sarkin Misau da wasu Sarakuna guda 2 a jihar

0
509

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya dakatar da Sarkin Misau, Ahmed Sulaiman, akan rikicin da yayi sanadiyyar mutuwar mutane tara a kauyen Hardawa dake karamar hukumar Misau.

A rahoton da Punch ta fitar, bayan shi gwamnan ya dakatar da wasu masu Sarautar gargajiyar guda biyu da suka hada da Hakimin Chiromah da kuma Mai Garin Zadawa.

A ranar Talata ne dai, gwamnan ya dakatar da shugaban karamar hukumar Misau na rikon kwarya, Yaro Gwaram da mataimakinsa, Baidu Kafin-Misau tare da sakataren shi, Usman Abdu.

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon fili da makiyaya suka shafe shekaru suna kiwo a wajen duk kuwa da cewa filin na gwamnati ne.

Gwamnati dai tana kokarin mayar da filin ya zama wajen noma ne, inda hakan ya kasa haifar da da mai ido a wajen makiyayan.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here