Yanzu-yanzu: Gobara ta kama a fadar shugaban kasa

0
12103

Gobara ta kama a fadar shugaban kasa dake Abuja a ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Babban mai bawa shugaban kasa shawara a fanin sadarwa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa wutar ba ta yi barna da yawa ba.

Garba Shehu ya bayyana cewa wutar ta kama ne sanadiyyar haduwar wayar wutar lantarki.

Garba ya ce lamarin ya faru a ranar Alhamis da yamma a wani shago kusa da dakin majalisa dake fadar shugaban kasar.

Ya ce: “Wutar ta kama, sanadiyyar haduwar wayar wutar lantarki, amma cikin gaggawa ma’aikatan cikin fadar shugaban kasar suka kashe wutar tun kafin zuwa masu aikin kashe gobara.

“Cikin sa’a ba tayi wata barna ba da yawa,” cewar Malam Garba Shehu.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here