Yanzu-yanzu: Fadar shugaban kasa ta dakatar da Ibrahim Magu daga shugabancin hukumar EFCC

0
658

A wani rahoto da muke samu yanzu, ya nuna cewa fadar shugaban kasar Najeriya ta dakatar da shugaban hukumar cin hanci da rashawa ta Najeriya, Ibrahim Magu daga kujerarsa.

Kamar yadda BBC ta ruwaito wata majiya mai tushe daga fadar shugaban kasa da ta bukaci a boye sunanta, ita ce ta tabbatar da haka a yau Talatar nan.

Idan ba a manta ba a jiya Litinin ne dai shugaban hukumar Ibrahim Magu ya bayyana a gaban kwamitin bincike wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa akan zargin da ake wa shugaban na aikata wasu abubuwa da suka sabawa gwamnati.

Kwamitin wacce tsohon mai shari’a Ayo Salami yake shugabanta, ta gayyaci Ibrahim a jiya domin jin ta bakinsa dangane da zargin da ake yi masa kan yadda yake tafiyar da mulki a hukumar ta EFCC.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here