Yanzu-yanzu: An nada Ganduje shugaban kwamitin yakin zaben gwamnan jihar Edo a APC

0
403

Kwamitin rikon kwarya ta babbar jam’iyya mai mulki, wato APC, wacce gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni yake jagoranta, ta nada wata kwamiti ta mutane 49 don yakin neman zaben gwamnan jihar Edo.

A ranar 19 ga watan Satumbar wannan shekarar ne dai za a gabatar da zaben.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, shine aka bawa shugabancin wannan kwamiti, inda gwamnan jihar Imo kuma Hope Uzodinma zai taimaka masa a matsayin mataimaki, sai kuma Abbas Braimoh a matsayin sakataren kwamiti.

A ranar 6 ga watan Yulin nan ne dai za a rantsar da ‘yan kwamitin, kamar yadda mataimakin kakakin jam’iyyar na kasa ya bayyana a sakatariyar jam’iyyar dake babban birnin tarayya.

Osaze Ize-Iyanmu shine dan takarar jam’iyyar APC wanda zai kara da Godwin Obaseki na jam’iyyar PDP, bayan rikicin siyasa da ya shiga tsakaninsu.

Ga dai jerin ‘yan kwamitin a kasa:

 1. Dr. Abdullahi Umar Ganduje – Shugaba
 2. (Sen.) Hope Uzodinma – Mataimakin shugaba
 3. Sen. Ovie Omo-Agege – Mamba
 4. H.E. Inuwa Yahaya – Mamba
 5. H.E. Alh. Yahaya Bello – Mamba
 6. H.E. Babajide Sanwo-Olu – Mamba
 7. H.E. (Chief) John Odigie-Oyegun – Mamba
 8. H.E. Comrade Adams Oshiomhole – Mamba
 9. Sen. Aliyu Magatakarda Wamakko – Mamba
 10. H.E. Sen. Godswill Akpabio – Mamba
 11. H.E. Sen. Orji Uzor Kalu – Mamba
 12. H.E. Sen. Owelle Roachas Okorocha – Mamba
 13. H.E. Timipre Sylva – Mamba
 14. H.E. Dr. Pius Odubu – Mamba
 15. Sen. Degi Eremiemyo Biobaraku – Mamba
 16. H.E. Prof. Oserheimen A. Osunbor – Mamba
 17. H.E. Emmanuel Eweta Uduaghan -Mamba
 18. Sen. John Owan Enoh – Mamba
 19. Rt. Hon. E.J. Agbonayiman – Mamba
 20. Engr. Babachir Lawal – Mamba
 21. Prince B.B. Apugo – Mamba
 22. Gen. Charles Airhiavbere – Mamba
 23. Hon. Peter Akpatason – Mamba
 24. Hon. Patrick Alsowleren – Mamba
 25. Hon. Johnson Oghuma – Mamba
 26. Hon. Prof. Julius Ihonvbere – Mamba
 27. Hon. Pally Iriase – Mamba
 28. Hon. Dennis Idahosa – Mamba
 29. Mrs. Rachel Akpabio – Mamba
 30. Mr. Bolaji Afeez – Mamba
 31. Engr. Gabriel Iduseri – Mamba
 32. Chief Cairo Ojougboh – Mamba
 33. Patrick Obahiagbon – Mamba
 34. Chief Ayiri Emami – Mamba
 35. Hon. Abubakar Adagu Suberu – Mamba
 36. Usman Nahuche – Mamba
 37. Engr. Chidi Orji – Mamba
 38. Dr. Almajiri Giadam – Mamba
 39. Sen. Sa’idu Umar Kumo – Mamba
 40. Chief Pius Akinyelure – Mamba
 41. Engr. Chris Ogiemwonyi – Mamba
 42. Chief Solomon Edebiri – Mamba
 43. Prof. Ebegue Amadasun – Mamba
 44. Hon. Saturday Uwulekue – Mamba
 45. Hon. Osaro Obaze – Mamba
 46. Chief Samuel Ogbuku – Mamba
 47. Miss. Rinsola Abiola – Mamba
 48. Theresa Tekenel – Mamba
 49. Hon. Abbas Braimoh – Sakatare

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here