Yanzu-yanzu: An kashe shugaban jam’iyyar APC a jihar Katsina

0
5624

An kashe shugaban jam’iyyar APC mai mulki na karamar hukumar Batsari, Abdulhamid Sani Ruma a kauyensu.

An ruwaito cewa Ruma ya tafi kauyensu na Sabon Garin Dunburawa don ya halarci wani taro na danginsu, inda aka harbe shi da yawa a can.

Wata majiya ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun fito daga cikin daji ne suka bude masa wuta, inda ya mutu a take a wajen.

Daga baya an kai gawarshi babban asibitin Batsari, inda aka bayyana cewar ya mutu a asibitin.

“Marigayin ya tafi kauyensu yau da safe da misalin karfe 9 na safe daga gidansa dake nan Batsari. Daga nan zuwa kauyen tafiyar kilomita hudu ce kawai. An harbe shi a hanya,” cewar majiyar da ta yiwa Daily Trust bayani.

Mataimakin shugaban jam’iyyar, Mamman Yaro Batsari shine ya bayyana mutuwar tashi.

Ya ce kashe shugaban jam’iyyar da har yanzu ba a san wanda yayi ba ya jefa garin cikin damuwa.

Ya ce; “Shekarar da ta gabata wadannan ‘yan bindigar sun kashe dan uwanshi, wannan shekarar kuma da ake shirin shiga lokacin damuna, sai aka kira shi a kauyensu domin yaje ya sanya ido akan rabon gadon dan uwanshi da za’ayi.”

“A lokacin da yake hanyar zuwa kauyen, ‘yan bindigar sun fito daga daji suka bude masa wuta, inda harsashi ya fasa kanshi da kirjin shi.”

“Maganar nan da nake yi daku yanzu, an kai gawarsa kauyensu domin yi masa jana’iza,” ya kara da cewa.

Rundunar ‘yan sandan jihar dai har yanzu bata yi magana akan lamarin ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here