Yanzu-yanzu: An garzaya da Sarkin Rano zuwa asibiti babu lafiya

0
130

Daya daga cikin sababbin Sarakunan yanka guda biyar da aka kirkira a jihar Kano, Sarkin Rano, Mai Martaba, Dr Tafida Abubakar Ila II, an ruwaito cewa an garzaya dashi zuwa asibiti a jiya Juma’a 1 ga watan Mayu, sanadiyyar rashin lafiya.

Duk da dai har yanzu ba a bayyana ko rashin lafiyar tashi na da nasaba da cutar Coronavirus ba, amma jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an kai shi asibitin koyarwa na Aminu Kano a cikin mawuyacin hali.

Daga nan an bukaci a kai shi asibitin Nasarawa domin duba lafiyarsa.

Daya daga cikin masu mukamin gargajiya a masarautar ta Rano, wanda ya nemi a boye sunansa, shine ya bayyanawa manema labaran cewa an garzaya da Sarkin zuwa asibitin koyarwa na Aminu Kano, amma daga baya an bukaci a kai shi asibitin Nasarawa.

Ya ce: “Mota dauke da Sarkin Rano ta nufi asibitin Nasarawa daga asibitin koyarwa na Aminu Kano, Sarkin na cikin wani mawuyacin hali a lokacin da suka bar asibitin Aminu Kano.

“Sarkin na cikin mawuyacin hali, Allah ya kare mu baki daya. Amin.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here