‘Yan Shi’a sun ci mutuncin Anas Ibn Malik (RA), yayin da suka hau kan kabarinsa suke zagin shi

0
383

Wasu matasan ‘yan Shi’a dake kasar Iraqi sun ci zarafin Khalifa Anas Ibn Malik (RA), yayin da suka hau kan kabarinsa suka fara zagin shi.

Kasar Iraqi wacce take ita ce kasa ta biyu da take da yawan ‘yan Shi’a bayan kasar Iran, ana zargin su da cin zarafin kabarin Anas Ibn Malik din, bayan an nuno su a sabon bidiyo suna daukar kansu a lokacin da suke yin wannan aika-aika.

Labarin dai wata kafar yada labarai ce ta kasar Pakistan mai suna News 92 ta wallafa, inda ta nan ne wanna bidiyo ya yadu a duniya, manyan kasashen Musulmai na duniya dai sun fara tilasta shugabannin kasar Iraqi akan su kama wadannan yaran, kamar yadda aka nuna a bidiyo.

Kamar yadda kowa ya sani, Anas Ibn Malik (RA), ya ruwaito Hadisai masu yawan gaske na Manzon Allah (SAW), babban Sahabi ne na Annabi, kuma dan uwa ne ga Annabi Muhammad (SAW).

Bayan fitar wannan labari dai, Musulmi da yawa na duniya hankalinsu ya tashi, ganin yadda matasa ‘yan asalin kasar Iraqi suna ciwa kabarin Sahabin Annabi mutunci.

Malamai da yawa sun sanar da Iraqi kamar yadda aka gani a bidiyon, cewa Iraqi tuni tana wani hali, kuma yin irin wannan cin zarafi ba zai taimaka musu ba.

Kabarin shi dai yana Basra ne, A lokacin da Annabi Muhammad (SAW) ya isa Madina a shekarar 622, mahaifiyar Anas Ibn Malik (RA), ta gabatar da shi ga Manzon Allah a matsayin wanda zai taimaka masa.

Yana daya daga cikin manyan Sahabban Manzon Allah da suka yi suna sosai a duniya, ya rasu a shekarar 93AH, a Basra a lokacin da yake da shekaru 103.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here