‘Yan sanda sun sake rufe sakatariyar jam’iyyar APC ta kasa dake Abuja

0
287

‘Yan sanda sun sake rufe sakatareriyar jam’iyyar APC, gabanin taron majalisar zartawa ta kasa (NEC) a yau.

‘Yan sandan sun ajiye manyan motoci guda biyu masu kirar Toyota Hilux da kuma guda biyu masu kirar Peugeot 604, da misalin karfe 9 na safe a kusa helkwatar jam’iyyar dake Abuja.

Jami’an tsaron sun umarci ma’aikatan wajen da suka fito wajen aiki da wuri sun bukaci da su fita daga wajen.

A ranar Laraba ne, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya goyi bayan Cif Victor Giadom, a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa, inda yayi watsi da Sen. Abiola Ajimobi a matsayin shugaban jam’iyyar.

A daren jiya ne, Ajimobi ya ce yana ganin cewa akwai yiwuwar an bawa shugaban kasar shawara marar kyau akan ya goyi bayan kwamitin zartarwar.

A cikin wata sanarwa da kwamitin ta fitar da sa hannun shugaban jam’iyyar na rikon kwarya, Prince Hilliard Eta, da kuma sakataren jam’iyyar na kasa mai rikon kwarya, Arc. Waziri Bulama, sun yi watsi da gayyatar zuwa wajen taron da Cif Victor Giadom.

A ranar Talata ne dai ‘yan sanda suka kori duka ma’aikata da ‘yan jarida daga cikin helkwatar jam’iyyar, kafin a fitar da sanarwar cewar an dauki wannan mataki domin wanzar da zaman lafiya.

Jam’iyyar APC din dai ta fada cikin rikicin jam’iyya tun makon da ya gabata, bayan dakatar da shugaban jam’iyyar na kasa Comrade Adams Oshiohmole a matsayin shugaban jam’iyyar na kasa, sannan aka tsayar da Giadom a matsayin shugaba mai rikon kwarya na tsawon mako biyu.

Sai dai kuma yawancin mambobin kwamitin NWC, din sun nuna goyon bayansu ga mataimakin shugaban jam’iyyar, Sen. Ajimobi, a matsayin shugaban na rikon kwarya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here