‘Yan Najeriya sun amince da coronavirus ne kawai saboda babu yadda suka iya, amma ba gaskiya ba ce – Yahaya Bello

1
2369

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa an kakabawa ‘yan Najeriya coronavirus ta dole ne, shine yasa suka yadda suka amince.

Gwamnan jihar Kogin ya bayyana hakane a wajen addu’ar marigayi Nasir Ajana, alkalin alkalai na jihar, wacce aka yi a yau Talata 30 ga watan Yuni.

Ya bayyana cewa annobar coronavirus an kawo ta ne kawai domin ta sanya tsoro, fargaba, sannan ta rage yawan shekarun al’umma.

Bello wanda ya musanta cewa marigayi tsohon alkalin alkalan ya mutu sakamakon cutar coronavirus ne, ya ce babu abinda yake kashe mutum da gaggawa fiye da tsoro da fargaba.

Ya ce:

“Koda masana lafiya da masana kimiyya sun yadda ko basu yadda ba, COVID-19 an kawo ta ne domin ta rage yawan shekarun al’umma, cuta ce da aka kakabawa ‘yan Najeriya ta dole akan babu yadda suka iya, kuma dole ta sanya suka yadda suka amince.

“Cutar COVID-19 an kawo ta ne kawai don a sanyawa mutane tsoro da fargaba, sannan kuma ta rage yawan shekarun da mutane ke yi a duniya.”

Wannan dai na zuwa ne yayin da hukumar lafiya ta Najeriya ta bayyana cewa sama da mutum 25,000 sun kamu da cutar a Najeriya.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here