‘Yan Najeriya na samun wutar awa 18 zuwa 24 a kowacce rana yanzu – Ministan wuta

4
5363

Ministan wutar lantarki, Sale Mamman, ya ce yanzu ‘yan Najeriya suna samun wutar lantarki ta awa 18 zuwa 24 a kowacce rana.

A wata hira da yayi da NTA, Mamman ya bayyana cewa gwamnatin Buhari ta kawo cigaba a fannin wutar lantarki ta hanyar karata zuwa 330KVA, wanda ita ce mafi karfi da aka taba samu a Najeriya.

Ya tabbatar da cewa tashoshin wuta 132 tuni an gyara su kuma an kammala tashar wuta ta Kashimbilla mai 40MW.

A cewar shi, aikin tashar wuta ta Zungeru dake jihar Neja tuni ta kai kashi 70 yanzu.

Da yake magana akan Mambilla kuwa, ministan ya ce sun gabatar da bincike, kuma sun gano cewa ma’aikata za su fara aiki nan ba da dadewa ba.

“Mun karfafa ayyukan mu, gwamnatin da ta wuce tana bawa mutane wutar lantarki ta kasa da awa goma a kowacce rana, amma a yau ina gaya muku muna bayar da wutar lantarki ta awa 18 zuwa 24 a kowacce rana.”

Mamman ya ce a baya Najeriya na da kasa da 3,000MW na wutar lantarki.

“Amma a yau, mun samar da 5,500MW, duk da dai baza mu iya bayar da duka ba saboda wasu dalilai.”

Ya tabbatar da cewar wutar lantarkin za ta cigaba da karfafa a Najeriya idan kamfanin Siemens AG na kasar Jamus suka fara aiki a kasar.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

4 COMMENTS

  1. A gaskiya mu mutanen borno state muna samun wuta kusan 24h muna mika godiyanmu ta musan man zuwa ga shugaban kasa da minister wutan lentarki dama ma aikatan wutan lentarki gabaki yasa

  2. Idan kai kana prime area ko wutar lantarkin ka na kan blue line dan kafadi hakan bakay karya ba amma fa akwai unguwanni mafiya yawa da wutar lantarkin awa shida zuwa tara suke samu. Manyan idan zakuy managar da ta shafi talakawa kurinka duba talakawan asali ba mawadata ba kokuma wanda kukey ma kirari da talakawa kahin a fitarda sanarwa

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here