‘Yan fim kunci amanar talakawa da masoyanku – Sakon Jaruma Rahama Hassan

0
861

Bayan shafe dogon lokaci ba tare da anji duriyarta ba, Jaruma Rahama Hassan ta aika da budaddiyar wasika ga abokan sana’arta na Kannywood a shafinta na Facebook.

Jarumar ta caccaki ‘yan fim da sauran mutanen da suka taya jam’iyyar APC tallata shugaban kasa Muhammadu Buhari neman takara a zango na biyu.

Rahama ta ce jaruman sunyi amfani da soyayyar da talakawa suke yi musu sun sanya su sun zabi shugaban kasa a shekarar da ta gabata.

Ta kara da cewa idan har da gaske jaruman suke yi sun yi wannan abu ne domin talakawa da kuma cigaban kasa, kamata yayi su fito su sanarwa da shugaban kasa halin da talakawan Najeriya ke ciki a fannin tsaro.

Jarumar ta ce suyi amfani da shafukansu na sadarwa wadanda suka taya shi yakin neman zabe dasu su yi kira ga shugaban kasar akan halin da ake ciki.

Ta ce a yanzu haka akwai kauyuka da yawa wadanda basa iya bacci idan dare yayi saboda tsoro da fargabar abinda ka iya biyo baya cikin dare na harin ‘yan bindiga.

Rahama ta cewa jaruman tabbas idan basu yi haka to wallahi sun ci amanar talakawan Najeriya da masoyan su da suka sanya suka zabi Buhari.

A karshe tsohuwar jarumar tayi addu’ar Allah ya kawo karshen wannan masifa, ya kuma zaunar da Najeriya lafiya.

Gareku Yan Kanywood da duk wasu mashhuren Mutanen da suka taya Jam'iyar Apc Tallata Mai Girma Shugaban Kasa na neman…

Posted by Rahama Hassan on Tuesday, June 16, 2020

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here