‘Yan daba sun shiga makabarta sun tono gawar shugaban karamar hukuma da Coronavirus ta kashe

3
10344

An tono gawar marigayi shugaban karamar hukumar Asari-Toru, Odiari Princewill, wanda ya mutu a jihar Rivers sanadiyyar cutar coronavirus.

‘Yan bindiga ne suka tono gawar marigayin, wadanda ake tunanin ‘yan asalin kauyen da ya fito ne.

Wasu da lamarin ya faru akan idonsu sun ce ‘yan bindigar sun shiga makabarta ta Fatakwal, inda suka dinga harbi babu kakkautawa a iska, suka nufi inda aka binne shugaban karamar hukumar suka tono akwatin da aka binne shi a ciki.

An ruwaito cewa sun gudu da gawar tashi daga wata barauniyar hanya da ruwa ke wucewa a garin na Fatakwal.

‘Ina ganin sun san wajen, domin kuwa yadda suka zo makabartar suka shiga a hankali. A lokuta da dama mukan samu mutane irin haka su zo musamman idan mutumin da ya mutu yana da wata kungiya ne.

“Amma wannan daban ne, sun zo kawai suka wuce makabarta kai tsaye suka fara hakar kabari. Su wajen 10 suka zo. Sun ce za su yiwa shugaban karamar hukumar binnewa ta musamman a mahaifarsa.” cewar shaidar wanda ya nemi a boye sunan shi.

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, DSP Nnamdi Omoni, yayi alkawarin bin diddigin lamarin.

Sai dai kuma wasu rahotanni daga Buguma kauyen da ‘yan bindigar suka kai gawar, ana ta faman rikici da jami’an tsaron da gwamnati ta aika don hana shiga da gawar cikin kauyen.

Marigayin Odiari Princewill, ya mutu a safiyar ranar Alhamis sanadiyyar cutar coronavirus da ta kashe shi, kuma an binne shi kamar yadda hukumar lafiya ta tanada a garin Fatakwal.

3 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here