‘Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace mutane 20 a Kaduna

0
275

Mutanen yankin Keke dake Kaduna Millennium City cikin karamar hukumar Chikun, sun tashi cikin tashin hankali bayan wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane biyu sun kuma sace mutane 20 a cikin daren ranar Lahadi.

Lamarin ya faru da misalin karfe 8 na daren ranar, a cewar mazaunan yankin, wadanda suka ce ‘yan bindigar sun shiga sanye da kayan sojoji dana ‘yan sanda, suka sanya shinge akan babbar gadar da za ta kai mutane cikin garin.

Wani mazaunin yankin wanda ya bayyana sunansa da Malam Kasimu Keke, ya sanar da wakilin Daily Trust, cewa yawancin wadanda lamarin ya shafa suna kan hanyar shigowa cikin gari ne, sai ‘yan bindigar suka tare su akan hanya.

“Sun zo da kayan sojoji da ‘yan sanda, sai suka sanya shing akan gadar da mutane ke bi idan za su shigo cikin gari, inda suka dinga tare mutane a ababen hawa.

“Direbobi da yawa sun tsaya suna tunanin cewa jami’an tsaro ne, amma wani mai shagon sayar da kaya, mai suna Ibrahim, sun harbe shi a take a wajen a lokacin da ya fara zargin cewa ‘yan bindiga ne.

“Sun kuma sake harbe wani mutumi a wajen, inda suka zama su biyu,” ya ce.

An yi kokarin jin ta bakin jami’an hukumar ‘yan sanda na jihar Kaduna, amma ba a cimma nasara, yayin da jami’in hulda da jama’a na hukumar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, bai daga wayar shi ba.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here