‘Yan bindiga sun kashe Kyaftin din soji, sun sace mahaifiyarshi da matarshi

0
405

A ranar Lahadin da ta gabata ne, wasu ‘yan bindiga suka harbe babban jami’in soja, dake a barikin sojoji ta Ojo Barracks dake jihar Legas, akan babbar hanyar Okene zuwa Lokoja.

Kyaftin GSM Abubakar, mai lamba N/13600, an ruwaito cewa yana tafiya a cikin motarsa mai kirar Honda Accord, sai ya hadu da ‘yan bindigar akan hanyarshi.

Wata majiya ta bayyana cewa Abubakar na dawowa daga jihar Legas ne zuwa makarantar sojoji ta Jaji dake jihar Kaduna, don shiga kwas din kananan jami’o’i da za a gabatar a wannan shekarar.

An ruwaito cewa yana tafiya tare da mahaifiyarsa da matarsa ne a lokacin da lamarin ya faru.

‘Yan bindigar sun budewa jami’in sojan wuta wanda ke sanye da manyan kaya, inda ya mutu a take a wajen.

Daga baya suka sace mahaifiyarsa da matarsa.

Wasu jami’an sojin dake cikin wata motar suna bin shi a baya suma da kyar suka sha.

An kai gawar jami’in zuwa cibiyar lafiya ta tarayya dake Lokoja, inda a ranar Talata danginshi suka je suka karbo shi don yi masa sallah kuma su binne shi, a jihar Neja.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka:

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

YouTube: https://www.youtube.com/channel/UCIHoX2u7YsETQz4_SM4RuEA

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here