‘Yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Adamawa yayin da ake jana’izar gawarwaki 38

0
160

A ranar Asabar ne ‘yan bindiga suka kai mummunan hari wani kauye dake jihar Adamawa, bayan an gama wani rikici da ya barke a garin ranar Juma’a tsakanin kabilar Hausawa da Chabo, a Tigno, karamar hukumar Lamurde.

Harin da aka kai ranar Asabar din an ruwaito cewa ya faru a Mbemun, da kuma Lamurde.

Mutanen garin sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kai hari garin suka sanyawa gidajen mutane wuta.

Amma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Suleiman Nguroje, ya ce tuni an aika jami’an ‘yan sanda yankin don tabbatar da tsaro.

Mazauna ‘yankin sun bayyanawa Daily Trust a ranar Lahadi cewa ranar Asabar sun binne mutane 38 kuma mutanen gari da jami’an tsaro sun shiga daji suna neman sauran gawarwakin wasu.

Wani da lamarin ya faru a gabanshi yace, rikicin ya samo asali ne bayan musu ya barke tsakanin wani dan kabilar Chabo da Bahaushe.

A lokacin da gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya kai ziyara garin tare da jami’an tsaro a ranar Juma’a bayan rikicin ya lafa.

Da yake magana a lokacin ziyarar tashi, Fintiri ya nuna rashin jin dadinsa sosai akan wannan abu da ya faru, inda yace tuni an sanya jami’an tsaro a yankin domin su tabbatar da tsaro a yankin.

Gwamnan ya bayyana rikicin a matsayin rikicin kasuwanci da manoma, inda ya bukaci al’ummar yankin da su zauna lafiya da juna.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here