‘Yan bindiga na gudowa daga jihohin Zamfara da Katsina suna shigowa jihar Neja – Sani Bello

0
1657

Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, ya danganta hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a wasu kananan hukumomi na jihar na da dangantaka da aika jami’an tsaro da aka yi jihohin Katsina da Zamfara.

Gwamnan wanda yake shine shugaban gwamnonin kungiyar Arewa ta Tsakiya, ya roki mutanen jihar musamman wadanda ke wuraren da lamarin ya shafa da su kwantar da hankulansu, PR Nigeria ta ruwaito.

Gwamnan ya bayyana hakane a lokacin da yake magana da manema labarai a garin Minna akan sakamakon abubuwan da suka tattauna a taron da suka gabatar akan tsaro da shugabannin rundunonin tsaro na jihar.

Da yake tabbatar da kokarin da yake wajen kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu. Bello ya yiwa mutanen jihar alkawarin gwamnatinsa za tayi duk wani abinda ya kamata don ganin ta inganta tsaro a jihar.

Gwamnan kuma ya nuna rashin jin dadinsa akan matsalar tsaro, inda yace akwai matakai da aka dauka domin kawo karshen matsalar.

“Na damu matuka akan abinda yake faruwa, kuma mun fito da wasu matakai da zasu kawo mafita akan lamarin. Zamu bi duk wata hanya domin tabbatar da tsaro a jihar Neja,” ya ce.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan majalisar jihar ta kira gwamnan akan yayi bayani dangane da dalilin da yasa gwamnatinsa ta gaza.

A lokacin da ya bayyana a gabansu ranar Talata 16 ga watan Yuni, ‘yan majalisar jihar sun zargi gwamnatin jihar akan bata tabuka komai wajen kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu a jihar tun daga watan Nuwambar shekarar 2019.

Majalisar ta bayyana cewa gwamnatin kawai tana ware kudi kalilan ne wajen yaki da ta’addanci a jihar. Haka kuma a wajen wannan taro kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya halarta.

Domin cigaba da samun labaran mu kai tsaye a wayoyinku, zaku iya biyo jaridar Press Lives a shafukan sadarwa kamar haka: 

Facebook: https://www.facebook.com/pressliveshausa

Twitter: https://www.twitter.com/pressliveshausa

Ko kuma ku aiko mana da sako ko sharhi ta adireshin mu na Email kai tsaye info@presslives.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here